Wasanni-Kwallon kafa

Aubameyang ya rattaba hannu a sabon kwantiragi da Arsenal

Rage et soulagement pour le Gabonais Pierre-Emerick Aubameyang après avoir marqué contre Manchester United, dimanche 10 mars 2019.
Rage et soulagement pour le Gabonais Pierre-Emerick Aubameyang après avoir marqué contre Manchester United, dimanche 10 mars 2019. REUTERS/Eddie Keogh

Kyaftin din kungiyar kwallon kafar Arsenal Pierre-Emerick ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi a kungiyar bayan daukar dogon lokaci ana ko kwanton cigaba da zaman sa a kungiyar.

Talla

Dan wasan mai shekaru 31 ya sanar da kulla sabuwar kwangilar ta bidiyo daga filin wasan Emirate dake London.

A karshen makon da ya gabata Aubameyang ya jefa kwallo guda daga cikin guda 3 da Arsenal ta zirarawa kungiyar Fulham a was an farkon da kungiyar tayi a gasar Firimiya.

Aubameyang ya jefa kwallaye biyu a wasan karshe na cin kofin FA da Arsenal ta lashe a karawar da suka yi da Chelsea nasarar da ta baiwa kungiyar damar shiga gasar Europa da zai gudana nan gaba.

Dan wasan ya koma Arsenal ne daga kungiyar Borrussia Dortmund a shekarar 2018 ya kuma lashe takalmin zinare a gasar shekarar 2018-2019 saboda yawan kwallayen da ya ci.

A kakar da ta gabata, Aubameyang ya zo na biyu wajen jefa kwallaye a Firimiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI