Wasanni

Barcelona za ta zabtare albashin Messi

Lionel Messi
Lionel Messi REUTERS/Rafael Marchante

Shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu zai bukaci Lionel Messi da ya amince da matakin zabtare albashinsa kamar yadda jaridar Deportes Cuatro hta rawaito.

Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Mujallar Forbes ta bayyana Messi a matsayin dan wasan kwallon da ya fi samunn kudin shiga a bana.

Forbes ta kiyasta cewa Messi ya samu Dala miliyan 126 a shekara guda, yayin da Cristiano Ronaldo na Juventus ke matsayi na biyu da Dala miliyan 117.

Neymar na PSG na matsayi na uku da zunzurutun Dala miliyan 96 da ya samu a cikin shekara guda.

Sai Kylian Mbappe na PSG da ke matsayi na hudu da Dala miliyan 42, yayin da Mohd. Salah na Liverpool ke matsayi na biyar da Dala miliyan 37.

JERIN 'YAN WASAN KWALLON DA SUKA FI SAMUN KUDI A BANA

1.Lionel Messi (Barcelona da Argentina) $126m

2.Cristiano Ronaldo (Juventus da Portugal) $117m

3.Neymar (Paris St-Germain da Brazil) $96m

4.Kylian Mbappe (Paris St-Germain da Faransa) $42m

5.Mohamed Salah (Liverpool da Masar) $37m

6.Paul Pogba (Manchester United da Faransa) $34m

7.Antoine Griezmann (Barcelona da Faransa) $33m

8.Gareth Bale (Real Madrid da Wales) $29m

9.Robert Lewandowski (Bayern Munich da Poland) $28m

10.David de Gea (Manchester United da Sifaniya) $27m

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.