Wasanni

Chelsea za ta yi gogayya da Liverpool a kakar bana-Lampard

Frank Lampard
Frank Lampard Reuters

Kocin Chelsea Frank Lampard ya ce, kungiyarsa da aka sake wa fasali, dole ne ta kudirta yin gogayya da Liverpool mai rike da kofin firimiyar Ingila.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan wasan na Chelsea sun fara gasar firimiya da kafar dama, inda suka doke Brighton da kwallaye 3-1.

A kakar da ta gabata, Chelsea ta kammala gasar ta firimiya da tazarar maki 33 da Liverpool ta bata, sannan kuma ta gaza samun nasara a dukkanin haduwarta da Liverpool a wancan kaka.

To sai dai a wannan kaka da muke ciki, Chelsea din ta kashe kimanin Pam miliyan 200 wajen sayo zakakuran ‘yan wasa kamar Timo Werner da ta cefano shi daga RB Leipzig da kuma Kai Havertz daga Bayern Leverkusen.

Wadannan sabbin ‘yan wasa sun taka leda a karawar  da Chelsea da samu nasara a a kan Brighton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.