Wasanni-Kwallon kafa

Bale ya fi son komawa Tottenham - wakilinsa

Gareth Bale, dan wasan Real Madrid.
Gareth Bale, dan wasan Real Madrid. REUTERS/Andrea Comas

Wakilin dan wasan Real Madrid, Gareth Bale, Jonathan Barnett ya ce Real Madrid na cikin tattaunawa da Tottenham a kan komawar dan wasan gasar Firmiya.

Talla

A shekarare 2013 ne Bale ya bar Tottenham zuwa Madrid inda ya lashe kofin gasar zakarun nahiyar Turai har 4.

Dan wasan ya ci kwallaye 105 daga wasanni 251 da buga wa Madrid, ya kuma lashe kofin gasar La ligar Spain har biyu, bayan na zakarun Turan da ya ci.

Sai dai duk da wadannan nasarori, dangantaka tsakanin dan wasan gaban da kocin Real Madrid

Zinedine Zidane ta yi tsami, inda wasanni 16 ne kawai ya buga a kaka wasannin da ta gabata.

A wannan kaka, an sha sa ran Bale zai yi hannu riga da kungiyar da ya shafe shekaru 7 yana murza mata tamola, haka ma sau da dama kafin wannan kaka ana danganta shi da barin Madrid din.

A Talatar nan aka ce Manchestyer United da Tottenham sun nuna sha’awar dauko dan wasan, amma wakilinsa ya tabbatar da cewa Bale ya fi son komawa Tottenham, kungiyar da ya fara wa wasa a shekarar 2007, bayan ya baro Southampton.

Wakilin na sa ya ce Bale ya fi sha’awar komawa Tottenham, saboda har yanzu yana kaunar kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI