Wasanni-Kwallon kafa

Tsohon sakataren FIFA ya ce talauci ya mai kamun kazar kuku

Jérôme Valcke, tsohon sakataren FIFA.
Jérôme Valcke, tsohon sakataren FIFA. REUTERS/Sergio Moraes/

Tsohon sakatare janar na hukumar kwallon kafa ta duniya Jerome Valcke ya yi wa wata kotu a Switzerland korafi kan yadda yake fama da talauci tun da ya rasa aikinsa a FIFA, a matsayin nan hannun Sepp Blatter, tare da cewa yanzu haka ya sayar da karamin jirgin ruwansa, da sarkoki da agogunansa na gwalagwalai.

Talla

Valcke ya bayyana a gaban kotu ne a kwana na biyu na shari’ar da ake mai kan badakalar bayar da damammakin kallon wasanni a talabijin, wanda aka ce da shugaban kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain Nasser Al-Khelaifi ne suka hada baki.

Da hawarsa akwatin kotu, Valcke ya fara bayanin yadda ko karfanfana ba shi da ita saboda tsabagen talauci, tun da ya rasa aikinsa a shekarar 2015, ga kuma horon dakatarwa ta shekara 10 da aka kakaba mai.

Valcke ya ce yana cikin halin kakani kayi duba da cewa shi mai iyali ne ga shi kuma ba shi da aiki, kuma ko da ya samu kudi nan da nan suna karewa.

Bafaranshen mai shekaru 59 ya ce tun a shekarar 2017 ya kasa bude asusun banki a Turai, saboda haka a shekarar 2018 ya rabu da matarsa don ta samu ta iya bude asusu.

Sai dai ya ce ba zaman banza yake ba, saboda ya koma gona, kuma yana fata zai girbi amfani da zai samar mai da kudin shiga a watanni masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI