Wasanni-Coronavirus

Fannin kwallon kafa ya tafka hasarar dala biliyan 11 saboda coronavirus - FIFA

Shugaban FIFA, Gianni Infantino a kasar Austria. 4/9/2020.
Shugaban FIFA, Gianni Infantino a kasar Austria. 4/9/2020. JOE KLAMAR / AFP

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta ce annobar coronavirus ta janyowa fannin tamaular hasarar kudaden shiga da yawansu ya kai dala biliyan 11.

Talla

FIFA tace cutar ta haddasa tafka hasarar biliyoyin dalar ne ta hanyoyin, takaita yawan wasannin da za a buga a kakar wasan da ta kare, haramta cinikin tikitan kallon wasannin dalilin hana ‘yan kallo halartar filaye, sai kuma hasarar yarjejeniyoyin saida damar haska wasannin kai tsaye da hukumomin kwallon kafa da kafafen yada labarai gami da kamfanoni suka cimma.

Wannan rahoto shi ne irinsa na farko da hukumar ta FIFA ta bayyana kan tasirin da annobar ta coronavirus ta yi kan kwallon kafa a duniya tun bayan bullarta daga China a watan Disambar shekarar 2019.

FIFA tace yanzu haka hukumomin kwallon kafa sama da 150 ne daga sassan duniya suka nemi tallafi bashi, daga asusun gaggawa na dala biliyan 1 da rabi, da ta samar don ragewa hukumomin kasashen radadin annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI