Wasanni

An haramtawa Neymar buga wasanni 2

Dan wasan PSG, Neymar.
Dan wasan PSG, Neymar. AFP/Pool/David Ramos

Kwamitin ladabtarwar gasar Ligue 1 a Faransa, ya yanke hukuncin haramtawa tauraron kungiyar PSG Neymar buga wasanni 2, sakamakon hatsaniyar da aka same shi da laifin shiga yayin wasansu da Marseille a ranar Laraba, abinda ya kai ga korar shi daga wasan, bayan maka masa jan kati.

Talla

Kwamitin ladabtarwar ya kuma sanar da shirinsa na kaddamar da bincike kan zargin nuna wariyar launi yayin rikicin da ya kaure tsakanin ‘yan wasan na PSG da Marseille a wasan na ranar Laraba.

A wani labarin kuma, kwallon da dan wasan gaba na kungiyar ta PSG Julian Draxler ya jefa a ragar Metz yayin fafatawarsu a mintunan karshe ranar Alhamis, ya baiwa PSG nasarar farko a sabuwar kakar wasa ta Ligue 1 dake Faransa.

Za a iya cewa PSG ba ta soma sabuwar kakar wasan ta bana da kafar dam aba, la’akari da cewa, rashin nasara ta yi a dukkanin wasanni biyu da ta soma fafatawa da Lens da kuma Marseille, wadanda ta yi rashin nasarar a hannun kowannensu da kwallaye 1 da nema.

Tarihi ya nuna cewar rabon da PSG ta fuskanci irin wannan shan kaye a gasar Ligue 1 tun kakar wasa ta shekarar 1984 zuwa 1985.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI