Bale zai wuce London don kammala cinikinsa
Wallafawa ranar:
Dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale ya shirya yin balaguro zuwa Ingila a wannan Juma’a domin kammala komawarsa Tottenham Hotspur mai buga gasar firimiyar Ingila.
Har yanzu ana kan tattaunawa kan yarjejeniyar komawar dan wasan na Wales mai shekaru 31 zuwa Tottenham akan aro
Ganawar da ake yi tsakanin kungiyoyin biyu na yin armashi, kuma muddin ta daure a haka, to babu shakka Bale zai yi balaguro zuwa birnin London.
Bale ya fuskanci koma-baya a Real Madrid yayin da rahotanni ke cewa, ko a jiya Alhamis, shi kadai ya yi atisayensa a daidai lokacin da yake dakon sakamakon tattaunawar sauya shekarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu