Wasanni

Setien ya maka Barcelona a kotu

Tsohon Kocin Barcelona Quique Setien.
Tsohon Kocin Barcelona Quique Setien. Reuters/Albert Gea

Tsohon kocin Barcelona Quique Setien ya shigar da kara a gaban kotu domin kalubalantar abin da ya kira rashin mutunta shi da kungiyar ta yi a yayin korarsa, inda ta maye gurbinsa da Ronald Koeman.

Talla

Cikin korafin da ya gabatar wa kotun, Setien ya ce Barcelona ba ta biya shi kudin sallama ba, don rage masa radadin rasa aikinsa ba tare da ya shirya ba, sai dai kawai sakon tabbatar da cewar korarsa ta yi, abin da ya ce ya saba wa yarjejeniyar da suka kulla a ranar 14 ga watan Janairun wannan shekara, lokacin da ya maye gurbin Ernesto Valverde.

Daga cikin rashin nasarorin da suka janyo wa Setien kora, akwai ficewa daga gasar cikin kofin zakarun nahiyar Turai bayan lallarsa da Bayern Munich ta yi wa Barcelona da 8-2, sai kuma gaza lashe kofin gasar la liga ta Spain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.