Wasanni

Dan Najeriya ya sauya salon wasan gasar Serie A

Napoli ta dauko Osimhen ne daga Lille ta Faransa
Napoli ta dauko Osimhen ne daga Lille ta Faransa AFP/JEAN-FRANCOIS MONIER

Victor Osimhen ya haska a wasansa na farko a matsayin dan wasan Napoli a jiya Lahadi, inda suka samu nasara kan Parma da kwallaye 2-0 a gasar Serie A.

Talla

A wannan kakar ce, dan wasan mai shekaru 21 kuma dan asalin Najeriya ya koma Napoli akan Euro miliyan 80 daga Lille, inda ya zamo dan wasa mafi tsada da kungiyar ta saya a tarihi, yayin da ya sha gaban ‘yan wasa da dama irinsu Gonzalo Higuain wajen tsada.

Napoli ta sayi Higuain ne akan Euro miliyan 39 kuma shi ne na biyu mafi tsada bayan Osimhen.

A yayin wasan na jiya, sai da aka shafe tsawon minti 45, wato zagayen farko, ba tare da an jefa kwallo a raga ba, amma Osimhen na shigowa ya sauya salon wasan, inda har ya taimaka wa Martens jefa kwallon farko a minti na 64.

Dan wasan na Najeriya ya kuma kai hare-haren kwallaye, amma dai hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.