Wasanni-Kwallon kafa

Akwai yiwuwar Gareth Bale ya haura shekara guda a Tottenham

Dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale da yanzu haka ke Tottenham a matsayin aro.
Dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale da yanzu haka ke Tottenham a matsayin aro. REUTERS/Andrea Comas

Dillalin Gareth Bale da yanzu haka ke can a Tottenham matsayin aro daga Real Madrid, Jonathan Barnet, ya ce da yiwuwar dan wasan ya wuce wa’adin shekara guda a tsohuwar kungiyar tasa, sabanin yadda aka daura yarjejeniya tsakanin kungiyoyin biyu.

Talla

A makon jiya ne dan wasan gaban na Real Madrid, Gareth Bale ya koma Tottenham matsayin aro na shekara guda, amma da sharadin tsohuwar kungiyar tasa da ya raba gari da ita a 2013 zuwa Madrid kan yuro miliyan 85 a matsayin dan wasa mafi tsada a wancan lokaci ta amince da kara wa’adin aron nasa.

Dillalin na Bale dan Wales mai shekaru 31, ya sanar da cewa matukar abubuwa suka tafi yadda su ke bukata, dan wasan zai ci gaba da taka leda a Tottenham na tsawon lokaci, la’akari da cewa shi ne Club din da ya fi kauna a duniyar kwallo.

Bale, wanda ko a 2019 ya yi kokarin raba gari da Madrid zuwa China, kawo yanzu kofunan gasa 13 ya yi nasarar dagewa da Club din a wasanni 171 da ya doka masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.