Wasanni-Kwallon kafa

Birtaniya ta janye shirin bai wa 'yan kallo damar fara shiga filin wasa

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya janye matakin bai wa ‘yan kallon kwallo damar halartar filayen wasannin Firimiya a ranar 1 ga watan oktoba mai kamawa, sakamakon matakan dakile cutar da ke shirin sake yaduwa a karo na biyu cikin nahiyar Turai.

Filin wasa na El Khalifa da ke birnin Doha na Qatar.
Filin wasa na El Khalifa da ke birnin Doha na Qatar. Mustafa ABUMUNES / AFP
Talla

Cikin jawabin da Johnson ya gabatar yau Talata, ya ce sai zuwa nan da watanni 6 masu zuwa ne za su duba yiwuwar bai wa ‘yan kallon damar fara shiga filaye, batun da kai tsaye zai shafi kungiyoyin kwallon kafar wadanda suka dogara da kudaden hannun ‘yan kallo wajen tafiyar da harkokinsu.

Bayanan bangaren lafiya ne dai ke gargadin yiwuwar sake tsanantar cutar a sassan kasar bayan fara shawo kanta a baya-bayan nan.

Tuni dai matakin Firaministan ya fara gamuwa da caccaka daga magoya bayan kwallo da ke ganin an dakile su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI