Wasanni

Bayern Munich ta lashe gasar Super Cup

'Yan wasan Bayern Munich yayin murnar jefa kwallo a ragar Sevilla
'Yan wasan Bayern Munich yayin murnar jefa kwallo a ragar Sevilla REUTERS/Laszlo Balogh

Kungiyar Bayern Munich ta lashe gasar Super Cup bayan doke Sevilla da kwallaye 2-1 a daren jiya Alhamis, yayin fafatwar da ta kai su ga karin lokaci na mintuna 30, bayan kammala 90 na al’ada suna kunnen doki 1-1.

Talla

Sevilla ce ta soma jefa kwallo a ragar Munich ta hannun dan wasanta Lucas Ocampos a bugun fanareti, kafin daga bisani Leon Goretzka na Munich ya maida wasan 1-1, yayinda kuma a mintuna 104 na karin lokaci Martinez da ya maye gurbin Goretzka ya jefa kwallo ta 2 a ragar Sevilla.

Gasar ta Super Cup dai itace ta hudu dakungiyar Bayern Munich ta lashe a wannan shekara, zalika tana da damar lashe karin ta 5 a ranar Laraba mai zuwa indaza ta fafata ta Borussia Dortmund, abokiyar hamayyarta a gasar Bundesliga.

Ana dai fafata wasan lashe gasar Super Cup ne tsakanin zakarar gasar cin kofin zakarun Turai ta Champions League d da kuma zakarar gasar Europa.

Wani abu kuma daya dauki hankali shi ne baiwa ‘yan kallo kimanin dubu 15 da 500 damar shiga filin wasan na Super Cup da ya gudana a birnin Budapest na Hungray.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.