'Yan wasan Kwara United 9 sun kamu da coronavirus
Wallafawa ranar:
Rahotanni daga Najeriya na cewa ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar Kwara United guda 9 sun kamu da cutar coronavirus, bayan da gwajin likitoci ya tabbatar da hakan.
Zuwa wannan lokaci dai jami’an kungiyar ta Kwara United basu ce komai kan lamarin ba, bisa hujjar cewar sun jiran samun rahoto hukumar cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC.
Gwaje gwajen da ake yiwa ‘yan wasa da jami’ansu a Najeriyar dai bangare ne na shirin hukumar LMC dake shirya gasar kwallon kafar kasar ta Premier lig, kafin soma sabuwar kakar wasa a bana.
Rahoton kamuwar ‘yan wasan Kwara United 9 da coronavirus na zuwa ne kwana guda bayan da gwajin likitoci ya gano cewar dukkanin ‘yan wasan Lobi Stars sun kamu da cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu