Wasanni-Kwallon kafa

Liverpool sun fi karfin Arsenal - Arteta

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta tare da Pep Guardiola Manajan Manchester City.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta tare da Pep Guardiola Manajan Manchester City. Getty Images

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce bai yi takaici sosai ba a game da lallasa tawagarsa da Liverpool suka yi da ci 3 da 1, saboda hakan na nuni da iri matsayin da ya kamata ‘yan wasansa su kai.

Talla

Kamar dai yadda aka sani, ‘yan Arsenal suka fara saka kwallo a ragar Liverpool ta hannun Alexandre Lacazette, bayan yayi amfani da damar da kuskuren Robertson ya samar, amma fa tawagar Liverpool ta baiwa Arsenal gwale gwale a filin Anfield.

Liverpool ba ta yi kasa a gwiwa ba har sai da ta farke kwallon, ta kuma kara wasu guda biyu, lamarin da ya sa aka tashi wasa 3 da 1.

Arteta bai tsaya wani boye boye ko kare kai ba a ganawar bayan wasa da ya yi da yan jarida, inda ya ce Liverpool ta baiwa tawagarsa rata.

Kocin na Arsenal wanda tsohon dan wasan tsakiya ne a kungiyar ya ce gaskiyar magana ita ce Liverpool sun fi karfin Arsenal.

Ya ce tawagar Liverpool ta birge shi da irin jajircewarta a lokacin da take kasa da kwallo daya, kuma matsayin da ya ke sha’awar ganin Arsenal kenan a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.