Wasanni

Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon bana

Robert Lewandowski
Robert Lewandowski REUTERS/Michael Dalder

Hukumar Kwallon Kafar Turai UEFA ta ayyana Robert Lewandowski na Bayern Munich a matsayin gwarzon dan wasan shekara bangaren maza.

Talla

Dan wasan dan asalin kasar Poland mai shekaru 32, ya doke abokin taka ledarsa a Bayern Munich wato Manuel Neuer da kuma dan wasan Manchester City Kevin de Bruyne wajen lashe kyautar.

Lewandowski ya zura kwallaye 55 a wasanni 47 da ya buga a kakar da ta gabata, yayin da ya jagoranci Bayern Munich wajen lashe kofin zakarun Turai da kuma kofin gasar Bundesliga ta Jamus.

An mika masa kyautar ce a yayin bikin fitar da jadawalin gasar zakarun Turai ta kakar bana a birni Geneva.

Daya cikin abubuwan da suka fi daukar hankali a zubin jadawalin shi ne yadda aka hada Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a rukunin G.

Ga cikakken jadawalin gasar ta zakarun Turai

Rukunin A: Bayern Munich, Atletico Madrid, Salzburg, Lokomotiv Moscow

Rukunin B: Real Madrid, Shakhtar Donetsk,Inter Milan,Borussia M/gladbach  

Rukunin C: Porto, Manchester City, Olympiakos, Marseille

Rukunin D: Liverpool, Ajax, Atalanta, Midtjylland

Rukunin E: Sevilla, Chelsea, FK Krasnodar, Rennes

Rukunin F: Zenit St Petersburg, Borussia Dortmund, Lazio, Bruges

Rukunin G: Juventus, Barcelona, Dynamo Kyiv, Ferencvaros

Rukunin H: Paris St-Germain, Manchester United, RB Leipzig, Istanbul Basaksehir

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.