kwallo

Muller ya kafa tarihin lashe kofuna a Jamus

Thomas Mueller, dan wasan Bayern Munich.
Thomas Mueller, dan wasan Bayern Munich. REUTERS/Andreas Gebert

Thomas Muller ya zama dan wasan da ya fi kowane dan wasa lashe kofuna a tarihin Jamus, bayan da Bayern Munich ta doke Borussia Dortmund a wasan Super Cup din Jamus a daren Laraba.

Talla

Joshua Kimmich ne ya ci kwallo daya a minti na 82nd, a filin wasa na Allianz Arena, kwallon da ta baiwa Bayern nasara 3-2 a kan Dortmund, wacce ita ta zo ta biyu a gasar Bundesligar bara.

Tun da farko, Corentin Tolisso da Muller sun sanya Bayern a kan gaba ta wajen cin kwallaye 2, amma Julian Brandt da Erling Haaland suka farke wa Dortmund kwallayen, kafin Kimmich ya kai Bayern gaci.

Sau 9 Muller ya ci kofin Bundsliga, kofin kalubalen Jamus na DFB-Pokal sau 6, na zakarun nahiyar Turai 2, kofin duniya 1 da kofin kungiyoyin duniya na world club cup 1, kofuna UEFA Super Cup 2, da kofunan German Super Cup 6.

Muller ya buge tarihin da dan wasan Jamus, Bastian Schweinsteiger ya kafa na dan wasan da ya fi kowane dan wasa cin kofuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.