Wasanni-Kwallon kafa

Vinicius ya ceto Real Madrid a hannun Valladolid

Vinicius Junior, dan wasan Real Madrid.
Vinicius Junior, dan wasan Real Madrid. REUTERS/Susana Vera

Vinicius Junior ya ceto Real Madrid da kyar a wasan da suka doke Real Valladolid da ci daya mai ban haushi a daren Laraba, a yayin da suke ci gaba da fuskantar kalubalen rashin kwallaye a farkon gasar La Ligar Spain.

Talla

A wasan farko da suka buga a gasar ta La Liga, Real Madrid sun sha dauri irin na huhun goro a hannun Real Sociedad, wadanda suka rike su har aka tashi baram baram babu ci.

Zalika a ranar Asabar da ta gabata, da kyar da jibin goshi Sergio Ramos ya cire wa Madrid kitse a wuta a wasan da suka gwabza da Real Betis inda ya ci bugun daga kai sai mai tsaron raga, aka tashi wasa 1-0.

Rashin jefa kwallo a raga ya yi wa Madrid barazanar rashin nasara a filinsu na Santiago Bernabeu, a daren Laraba, inda suka yi ta baras da damammakin saka kwallaye a raga.

Luka Modric, wanda rahotanni ke alakanta shi da komawa Manchester United ya baras da dammaki biyu masu kyau, har sai da Vinicius ya shigo bayan hutun rabin lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.