Jadawalin gasar zakarun Turai ya hada Ronaldo da Messi a matakin rukuni
Wallafawa ranar:
Hukumar UEFA ta fitar da sabon jadawalin gasar cin kofin zakarun Turai da ya kunshi kungiyoyi 24 a rukunin takwas daga A zuwa H.
Jadawalin na UEFA ya nuna cewa Rukunin A na dauke da zakarar gasar ta bara: Bayern Munich da Atletico Madrid da Lokomotiv Moscow da kuma Salzburg wadanda za su kara tare da fitar da zakaru 2 da za su tsallaka zagayen kungiyoyi 16.
Rukunin B kuwa kamar yadda jadawalin ya nuna na dauke da: Real Madrid kana Shaktar Donetsk da Inter Milan sannan Borussia Monchengladbach.
Sai rukunin C da ya kunshi: Porto da Manchester City da Olympiakos da Marseille.
Rukunin D ya kunshi: Liverpool da Ajax sannan Atalanta da Midtjylland.
Rukunin E: akwai Sevilla da Chelsea da FK Krasnador da kuma Rennes.
Rukunin F: ya hada da Zenit St Petersburg da Borussia Dortmund da Lazio da kuma Bruges.
Rukinin G wanda ake ganin zai fi daukar hankali ya hadar da: Juventus da Barcelona da Dynamo Kyiv da kuma Ferencvaros, a dai wannan rukunin za a hadu da Ronald da Messi yayinda shi ma Suarez zai tunkari tsohuwar kungiyar ta sa Barcelona bayan sauya sheka a wannan kaka.
Rukunin H kuma na karshe ya kunshi: PSG da Manchester United sai RP Leipzig da Istanbul Basaksehir.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu