Wasanni

Manchester United ta sayo Cavani

Edinson Cavani ya ki tsawaita zamansa a PSG
Edinson Cavani ya ki tsawaita zamansa a PSG REUTERS/Charles Platiau

Kungiyar Manchester United ta kulla kwantiragi da dan wasan gaba na kasar Uruguay, Edinson Cavani mai shekaru 33 domin taimaka mata dawo da martabarta a gasar firimiya da ta zakarun Turai.

Talla

Jaridar Daily Mail da ake wallafawa a Birtaniya ta ce yarjejeniyar ta kunshi biyan Cavani albashin Pam dubu 235 a  kowanne mako, kuma ana sa ran yi masa gwajin lafiyarsa nan da sa’oi 24 masu zuwa.

Cavani shi ne dan wasan gaba da ya fi zura wa kungiyar PSG kwallaye bayan kwashe shekaru 7 yana mata wasa, inda ya jefa kwallaye 200, kafin kungiyar ta rage amfani da shi a kakar da ta gabata saboda sayo Mauro Icadi.

Bayan karewar kwangilarsa a ranar 30 ga watan Yuni, Cavani ya ki tsawaita kwangilar abin da ya sa Manchester United ta neme shi.

Ya zuwa yanzu shi ne dan wasa na biyu da Manchester United ta saya, bayan Donny van de Beek daga kungiyar Ajax, yayin da take ci gaba da zawarcin Jadon Sancho daga Dortmund.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.