An ci mutuncin Liverpool da Manchester United
Wallafawa ranar:
Kocin Liverpool Jurgen Kloop ya bayyana cewa, kungiyarsa ta kafa wani irin mummunan tarihi bayan Aston Villa ta yi biji-biji da ita a karawar da bangarorin biyu suka yi a gasar firimiyar Ingila, yayin da ita ma Manchester United ta gamu da rana mafi muni karkashin kocinta, Ole Gunnar Solksjaer.
Liverpool ta sha kashi da kwallaye 7-2 kuma ita ce kungiya ta farko a tarihi mai rike da kambi da ta sha irin wannan lallarsa a gasar firimiyar tun bayan Sunderland wadda ita hakan ya taba cikawa da ita a shekarar 1953.
A yayin wasan na ranar Lahadi, Ollie Watkins ya jefa kwallaye uku shi kadai, yayin da Jack Grealish ya taimaka wajen zura kwallaye biyar.
Kodayake ana ganin cewa, rashin kwararren golan kungiyar wato Allison Becker da ke jinya, ya taimaka wajen bai wa Aston Villa damar zura kwallaye masu yawa a ragar Liverpool.
Kazalika kungiyar ta yi wasan ne ba tare da daya daga cikin zaratan ‘yan wasanta na gaba ba wato Sadio Mane wanda ke fama da cutar coronavirus.
A bangare guda, halin kocin Manchester United ya tashi matuka sakamakon lallasar da Tottenham ta yi musu da ci 6-1.
Jiya ta kasance rana mafi muni ga Solksjaer a matsayinsa na kocin Manchester United, yayin da kungiysara ta koma matsayi na 16 a teburin gasar.
A karon farko tun shekarar 1986, Manchester United ta yi rashin nasara a wasanninta guda biyu na farko a gidanta na Old Trafford a gasar firimiyar Ingila, kuma kocinta ya ce, abin kunya ne yadda suka sha irin wanann lallasar kuma laifin nasa a cewarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu