Wasanni-Kwallon kafa

Arteta ya cire Ozil daga tawagar Arsenal da za ta kara a wasannin Europa

Dan wasan Arsenal Mesut.
Dan wasan Arsenal Mesut. REUTERS/Eddie Keogh

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta ya cire dan wasan tsakiyar Club din Mesut Ozil daga jerin ‘yan wasan da za su taka leda a wasannin Europa da ke tunkaro tawagar.

Talla

Ozil dan Jamus mai shekaru 31 wanda rabon da ya taka leda a bangaren Arsenal tun cikin watan Maris yanzu haka makomarsa a Club din na cike da tarabbabi musamman bayanda Arteta ya maye gurbinsa da Thomas Partey sabon dan wasan da Arsenal ta sayo daga Atletico Madrid kan yuro miliyan 45 a ranar karshe ta kulle kasuwar musayar ‘yan wasa.

A ranar 22 ga watan nan ne Arsenal za ta fara wasanninta a rukunin B karkashin gasar ta Europa inda za ta kara da Rapid Vienna, inda tuni Arteta ya kuma cire William Saliba da Sokratis Papastathopoulos a wasannin ciki har da wanda Arsenal din za ta kara da Dundalk da kum Molde daga Norway a matakin rukunin na Europa.

Ozil wanda Arsenal ta saya a wancan lokaci matsayi dan wasa mafi tsada a tarihin Club din, ko a Talatar da ta gabata, ya nemi biyan albashin wani mutum da ke taka rawar mutumin mutumin Club don kayatar da ‘yan kallo bayan da Arsenal ta nemi raba gari duk da shafe shekaru 27 yana mata aiki.

Cikin sakon da Ozil ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce a shirye ya ce ya biya albashin mutum mutumin matukar zai ci gaba da kasancewa a Arsenal ko da ya ke tuni Sevilla mai doka gasar La Liga a Spain ta fara tattaunawa da mai taka rawar mutum mutumin don komawa kayatar da magoya bayanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.