Wasanni

Arsenal na son yakice Ozil da karfi

Arsenal na son sake zaman tattaunawa da dan wasan tsakiya na Jamus, Mesut Ozil mai shekaru 31 game da kawo karshen kwantiraginsa da kungiyar kafin sabuwar kasuwar  musayar ‘yan wasa a cikin watan Janairu mai zuwa.

Mesut Ozil
Mesut Ozil REUTERS/Eddie Keogh
Talla

Rahotanni sun ce, kungiar ta tuntubi dan wasan makwanni biyu da suka shude domin cimma matsaya da shi game da watanni tara da suka rage masa a kwantiraginsa, amma dai bangarorin biyu sun tashi baran-baran.

Jaidar Mail ta ce, Ozil ya shaida wa kungiyar cewa yana son a biya shi sauran kudinsa da ya kai Pam miliyan 13 kamar yadda aka zayyana a kwantiragin nasa.

Yanzu haka dai, Arsenal za ta sake sabon zama da dan wasan mai karbar Pam dubu 350 a kowanne mako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI