Wasanni

Ina mafarkin taka leda a Real Madrid-Pogba

Dan wasn Manchester United Paul Pogba ya bayyana cewa, yana burin taka leda a Real Madrid domin kuwa wannan ne mafarkinsa da yake fatar ya tabbata wata rana.

Paul Pogba
Paul Pogba Reuters/Jason Cairnduff
Talla

Kodayake dan wasan mai shekaru 27 ya ce, zai yi duk mai yiwuwa don ganin ya kai Manchester United matakin da ta cancanci kaiwa.

An dade ana rade-radin cewa, da wasan na Faransa zai raba gari da Manchester United wadda ta cefano shi akan Pam miliyan 89 a shekarar 2016.

A cikin wannan kakar ce kwantiragin dan wasan zai kawo karshe amma kungiyar za ta iya tsawaita masa zamansa da shekara guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI