Wasanni-Kwallon kafa

Ina koyi da Ronaldo - Mbappe

Kylian Mbappé dan wasan gaba na PSG.
Kylian Mbappé dan wasan gaba na PSG. Reuters/Eric Gaillard

Kylian Mbappe ya jinjina wa dan asan da yake matukar kauna, kuma yake kwaikwaya, Cristiano Ronaldo bayan da suka raba rana a wasan da kasarsa Farsansa ta fafata da Portugal a gasar Lig na kasashen Turai da suka tashi canjaras.

Talla

Duk da kokari da dagewa da ‘yan wasan gaban biyu suka yi daga dukkan bangarori, an tashi wasan ba kare bin damo.

Sai dai a yayin da ba a saka kwallo a raga ba, Mbappe da Ronaldo sun yi iya kokarinsu na kayatar da ‘yan kallo a wasan da kowannensu ya gwada bajinta da baiwar da Allah ya yi masa.

Mbappe ya sha bayyana yadda yake kaunar Cristiano Ronaldo, inda bayan wannan wasa ma ya hau dandalin sada zumunta yana jinjina ga Ronaldo, har ma yake bayyana shi a matsayin abin koyi a gareshi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI