Wasanni-Kwallon kafa

Messi ke lashe kofuna ba Guardiola ba - Magath

Barcelona ta lashe kofin zakarun nahiyar Turai har biyu a karkashin Pep Guardiola ne saboda hazakar Lionel Messi a cewar tsohon kocin Bayern Munich, Felix Magath.

Dan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi.
Dan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi. REUTERS/Waleed Ali
Talla

Kungiyar ta lashe kofin La Liga biyu a karon farko, da na Copa del Rey da zakarun nahiyar Turai a kakar wasan 2008 da 2009, wanda ita ce kakar Guardiola ta farko a Barcelona.

Bayan shekaru biyu kungiyar ta sake lashe kofin zakarun Turai, inda ta sake doke Manchester United a wasan karshe, abin da ya kasance lokaci mafi armashi a gare ta a tarihinta.

Guardiola wanda ya yi hannun riga da Barcelona a shekarar 2012, bayan lashe manyan kofuna 14, ya gaza lashe kofin Turai tun daga wannan lokaci.

Sau 3 yana lashe kofin Bundesliga a Bayern Munich, amma kuma ya sha kashi sau 3 a matakin kusa da karshe na gasar zakarun nahiyar Turai a hannun Real Madrid, Barcelona, da Atletico Madrid.

Haka zalika, ya samu gagarumar nasara tare da Manchester City, kungiyar da yake horarwa a halin yanzu, inda ya lashe kofin Firimiyar Ingila 2, na FA daya, da na EFL 3, amma har yanzu dai ya gaza ketarawa da su matakin daf da na kusa da karshe a gasar zakarun Turai.

Magath ya soki salon wasan Guardiola na rike kwallo, yana mai cewa ya yi mai rana a Barcelona ne kawai saboda tana da Messi, wanda ke yin katabus duk rintsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI