Wasanni-Kwallon kafa

Pogba ya bayyana sha'awar komawa Real Madrid

Dan wasan tsakiya na Manchester United, Paul Pogba.
Dan wasan tsakiya na Manchester United, Paul Pogba. Reuters

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na sha’awar dauko dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba, amma rahotanni na nuni da cewa hakan zai yiwu ne kawai idan mai horar da ‘Yan wasanta, Zinedine Zidane ya ci gaba da zama a Santiago Bernabeu.

Talla

Zidane dai baban masoyi ne na Pogba, wanda dan kasar Faransa ne, kuma ya nuna cewa a shirye yake ya dauke shi daga Old Trafford da zarar an bude kasuwar hada hadar ‘yan wasa a shekarar 2021.

A wannan mako, Paul Pogba ya fito karara ya bayyana sha’awar komawa Real Madrid, inda ya ce fatarsa kenan a ce ya murza leda a filin wasa na Estadio Santiago Bernabeu.

Sai dai sanya farashin Yuro miliyan 114 da Manchester United ta yi a kan Pogba ya sa Real Madrid ta janye daga batun sayen dan wasan.

Amma Pogba da Zinedine Zidane sun hadu, har sun tattauna yadda za su samo mafita a game da sauya shekar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.