Wasanni

Ronaldo da Mbappe sun kasa yin komai

Cristiano Ronaldo da Paul Pogba a yayin wasan na Nations League a birnin Paris.
Cristiano Ronaldo da Paul Pogba a yayin wasan na Nations League a birnin Paris. Gonzalo Fuentes/Reuters

Cristiano Ronaldo da Kylian Mbappe sun gaza jefa kwallo a raga a fafatawar da kasashensu na Portugal da Faransa suka yi a gasar cin kofin Nations League ta Turai a birnin Paris, inda suka tashi ba-kare-bin-damo.

Talla

Portugal wadda ke rike da kambin kasashen Turai ta gaza maimaita abin da ta yi Faransa a shekarar 2016, lokacin da ta yi mata ci daya mai ban haushi a wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Turai a filin wasa na Stade de France da ke birnin Paris.

Mbappe mai shekaru 21 ya barar da kyakkyawar damar da Faransa ta samu, inda ya nuna kwalliya har mai tsaren ragar Portugal, wato Rui Patricio ya tare kwallon.

Shi ma Ronaldo ya samu wata kyakkyawar dama a daidai lokacin da wasan ya kawo karshe, yayin da Hugo Lloris ya tare kwallon.

Kimanin ‘magoya bayan tawagar Faransa dubu 1 suka halarci wasan bayan an takaita yawansu saboda annobar coronavirus.

Ana kallon Faransa da Portugal a matsayin kasashen da suka yi wa takwarorinsu zarra a fagen tamaula a Turai, lura da cewa, Faransa ke rike da kambin duniya, yayin bda Portugal ke rike da kambin gasar Nations Legaue wadda ta lashe a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI