Wasanni

Cristiano Ronaldo ya kamu da coronavirus

Dan wasan Portugal mai taka leda a Juventus Cristiano Ronaldo ya harbu da cutar coronavirus kuma tuni ya killace kansa.

Cristiano Ronaldo.
Cristiano Ronaldo. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Hukumar Kwallon Kafar kasarsa ta Portugal ta ce, tuni dan wasan mai shekaru 35 ya killace kansa, amma yana cikin yanayi mai kyau ba tare da nuna manyan alamomin cutar ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da tawagar kwallon kafar Portugal za ta kece raini da Sweden a gobe Laraba gasar Nations League ta kasashen Turai.

Kazalika dan wasan ba zai samu damar buga wasan da kungiyarsa ta Juventus za ta yi da Crotone a gasar Serie A ba a ranar 17 ga watannan nan Oktoba, da kuma wasan da za ta yi da Dynamo Kiev a gasar zakarun Turai a ranar 20 ga watan na Oktoba.

Gwaji ya nuna cewa, sauran abokan taka ledarsa a tawagar ta Portugal basa dauke da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI