Wasanni-Coronavirus

Karin 'yan wasan Firimiya 5 sun kamu da Coronavirus

Jumulla dai yanzu haka akwai 'yan wasan Firimiya 14 da ke jinyar cutar ta Coronavirus.
Jumulla dai yanzu haka akwai 'yan wasan Firimiya 14 da ke jinyar cutar ta Coronavirus. REUTERS

Hukumar gudanarwar gasar Firimiyar Ingila ta sanar da samun ‘yan wasa 5 sabbin kamuwa da coronavirus bayan gwajin da ta yi musu tsakanin ranakun 5 zuwa 11 ga watan Oktoban da muke ciki.

Talla

A sanarwar da ta fita, hukumar ta Firimiya ta ce ta gwada jumullar ‘yan wasa dubu 1 da 128 da ke taka leda a kungiyoyin Firimiya 20 a ranakun 6.

Sanarwar ta ce ‘yan wasan 5 sabbin kamuwa da coronavirus yanzu haka za su killace kansu na tsawon kwanaki 10 don gudun shafawa wasu cutar.

Sanarwar dai ba ta fitar da sunan ‘yan wasan da suka kamu da cutar a baya bayan nan ba.

Ko a gwajin da Firimiyar ta yiwa ‘yan wasan tsakanin ranar 28 zuwa 4 ga watan Oktoba, sai da aka samu ‘yan wasan 9 da suka kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI