Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Ozil na Arsenal bai cancanci ci gaba da zama a benci ba - Wenger

Dan wasan tsakiya na kungiyar Arsenal, Mesut Ozil.
Dan wasan tsakiya na kungiyar Arsenal, Mesut Ozil. REUTERS/Edgar Su
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya ce ko shakka babu tsohuwar tawagar tasa ta shiga hannun da ya dace a yanzu kuma yana da kwarin gwiwar, Mikel Arteta wanda tsohon dan wasan tawagar ne ya kafa gagarumin tarihin kai kungiyar ga babban mataki.

Talla

Wenger wanda ya shafe tsawon shekaru 22 yana horar da Arsenal, yayin da ya ke amsa tambaya kan halin da Club din ke ciki bayan tafiyarsa, ya ce akwai abubuwan da ya yi danasanin kasancewarsu a tsawon lokacin da ya dauka yana horarwa ciki har da rashin sayen Cristiano Ronaldo da yanzu ke taka leda a Juventus.

Haka zalika tsohon mai horarwar Arsene Wenger ya ce duk da halin da Mesut Ozil ke ciki a yanzu bai kamata magoya bayan Arsenal da shi kansa Club din su manta irin sadaukarwa da kuma gudunmawar da ya bayar a lokutan baya ba, musamman kasancewarsa dan wasan tsakiya mafi taimakawa a zura kwallo da Club din ya taba samu a tarihi.

A cewar Arsene Wenger kamata ya yi Arsenal ta ci gaba da tafiya da Ozil tare da mayar da shi yadda ya ke a baya.

Kafin yanzu dai sabon mai horar da Kungiyar ta Arsenal Mikel Arteta y ace Ozil na fama da rashin sa’a, yayinda ya cire shi daga jerin ‘yan wasan Club din da za su fafata a wasannin Europa da ke tafe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.