Wasanni
Naymar ya kafa sabon tarihi a Brazil
Neymar na Brazil ya antaya kwallaye uku, wato hatrick a Turance a karawar da kasarsa ta doke Peru da ci 4-2 a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Wallafawa ranar:
Talla
Yanzu haka Neymar ya kafa tarihin zama dan wasa na biyu da ya fi ci wa Brazil kwallaye a tarihi, inda yake da kwallaye 64, yayin da yake biye da Pele wanda ke da kwallaye 77.
Neymar ya zarta Ronaldo a yanzu, inda ya ba shi ratar kwallaye biyu.
Dan wasan mai taka leda a PSG ta Faransa, ya buga wa Brazil wasanni har guda 103 kawo yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu