Wasanni

Ronaldo ya baro Portugal zuwa Italy bayan kamuwa da Coronavirus

Cristiano Ronaldo na Portugal da ke taka leda a Juventus.
Cristiano Ronaldo na Portugal da ke taka leda a Juventus. Susana Vera/Reuters

Fitaccen dan kwallon Duniya, Cristiano Ronaldo ya bar tawagar kungiyar kwallon kafar Portugal da ke Lisbon, domin komawa Italia inda zai ci gaba da jinyar cutar korona da aka gano yana dauke da ita.

Talla

Rahotanni sun ce dan wasan na Juventus ya bar tashar jiragen Lisbon ne yau da rana a cikin jirgin sa kamar yadda aka nuna ta gidan talabijin din CMTV kai tsaye.

Hukumar kwallon kafar Portugal ta sanar da harbuwar ‘dan wasan ranar litinin, kwana guda bayan ya buga wasan da kasar sa ta yi da Faransa a gasar cin kofin Turai da ake kira Nations League.

Abokin wasan sa a kungiyar Juventus Giorgio Chiellini ya ce ya yi magana da Ronaldo kuma yana cikin koshin lafiya.

Kafin karawar da suka yi a karshen mako, gwaji ya nuna cewar biyu daga cikin tawagar ‘yan wasan Portugal sun harbu da cutar da suka hada da golan kungiyar Lyon Anthony Lopes da dan wasan baya na kungiyar Lille, Jose Fonte.

Ronaldo shi ne fitaccen dan wasa na baya bayan nan da ya harbu da korona bayan Neymar da Kylian Mbappe da kuma Zlatan Ibrahimovic.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.