Wasanni

Spain ta sha kashi irinsa na farko cikin shekaru biyu

Viktor Tsygankov na Ukraine a tsakiyar Sergio Ramos da Dani Olmo na Spain
Viktor Tsygankov na Ukraine a tsakiyar Sergio Ramos da Dani Olmo na Spain Reuters

A karon farko cikin kusan shekaru biyu, tawagar kwallon kafar Spain ta sha kashi bayan da takwararta ta Ukraine ta yi mata ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin Nations League ta Turai.

Talla

A yayin wasan na jiya, Spain ta barar da damammakin da ta samu , yayin da ta kaddamar da hare-haren kwallaye har sau 21, amma hakarta ba ta cimma ruwa ba.

A minti na 76 ne, Ukraine ta yi amfani da dama daya tilo da ta samu har ta jefa kwallo a ragar Spain ta hannun Viktor Tsygankov wanda ya taso daga banci.

Alkaluma sun nuna cewa, Spain na da maki 72 wajen rike kwallo, yayin da Ukraine ke da maki 28.

Kimanin ‘yan kallo dubu 15 aka lamuncewa shiga filin wasan na birnin Kiev.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.