Wasanni

Juventus ka iya rabuwa da Ronaldo saboda Mbappe

Cristiano Ronaldo da Kylian Mbappe
Cristiano Ronaldo da Kylian Mbappe Mirror

Juventus na shirin ware Pam miliyan 360 domin dauko Kylian Mbappe daga Paris St-Germain ta Faransa, matakin da ke zama babban koma-baya ga Real Madrid da Liverpool da ke hankoron dauko dan wasan.

Talla

Jaridar Mirror ta ce, Juventus ka iya ajiye Cristiano Ronaldo a gefe domin bai wa Mbappe damar watayawa, yayin da ake kallon dan wasan a matsayin mafi daraja a duniyar tamaula a yanzu haka.

Muddin cinikin ya tabbata, ga alama Juventus za ta raba gari da Ronaldo domin kuwa ba za ta ci gaba da biyan makudan kudade ga 'yan wasan biyu ba a lokaci guda.

Ana ganin batun cinikayyar matashin dan wasan, shi ne zai mamaye kasuwar musayar 'yan wasa a kaka mai zuwa, yayin da dan wasan ya shaida wa PSG cewa, shi ma yana sha'awar sauya sheka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.