Wasanni

Ya kamata Manchester ta hutar da Maguire-Ferdinand

Harry Maguire na Manchester United tare da Jamie Vardy na  Leicester City a yayin wasan firimiya.
Harry Maguire na Manchester United tare da Jamie Vardy na Leicester City a yayin wasan firimiya. Pool via REUTERS/Michael Regan

Tsohon dan wasan Manchester United, Rio Ferdinand ya bayyana cewa, hutar da Harry Maguire ka iya amfanar da dan wasan .

Talla

An kori Maguire mai shekaru 27 daga kan fili a wasan da kasarsa ta Ingila ta yi da Denmark a ranar Laraba, yayin da dan wasan ke ci gaba da fafutukar ganin ya gyagije tun bayan da aka tsare shi a Girka gabanin shiga sabuwar kakar wasanni.

Kungiyarsa ta Mancheter United za ta yi wasanta na gaba da Newcastle a ranar Asabar , yayin da Ferdinand ke ganin cewa, ya kamata kungiyar ta hutar da dan wasan ko da kuwa na dan wani lokaci.

Ferdinand ya bayyana cewa, hutar da dan wasan ka iya ba shi damar maido da karsashinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.