Wasanni

Bale ya shiga Tottenham da kafar hagu

Gareth Bale
Gareth Bale Reuters

Sabon dan wasan Tottenham wanda ta dauko daga Real Madrid Gareth Bale ya gaza cire mata kitse a wuta a daidai lokacin da take cikin tsananin bukata, inda ya barar da wata kyakkyawar damar zura kwallo a ragar West Ham ana gab da tashi wasa.

Talla

A yayin da ya rage kiris a tashi wasan na ranar Lahadi a gasar firimiyar Ingila, Tottenham na samun nasara da ci 3-2 , amma Bale ya gaza amfani da kyakkyawar damar da ya samu ta zura kwallo ta hudu.

Shi kuwa Lanzini na West Ham ya yi amfani da  damar da shi ma ya samu ana gab da tashi wasan, inda ya zura kwallo a ragar Tottenham, abin da ya sa kungiyoyin biyu suka tashi canjaras 3-3.

West Ham ta yunkuro har ta farke dukkanin kwallayen uku cikin minti 10 da Tottenham ta zura mata.

Tottenham ta zura kwallayenta a minti na 1 da na 8 da kuma na 16, yayin da West Ham din ta farke a minti na 82 da 85 da kuma 94, ana gab da tashi wasan.

Ana ganin Bale ba zai taba mancewa da damar da ya barar ba a tarihinsa na taka leda a Tottenham, lura da cewa, wasansa ke nan na farko a kungiyar.

An sanya Bale cikin wasan ne a minti na 72 kuma a daidai lokacin da Tottenham ke kan jan ragamar wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.