Shirin Duniyar Wasanni tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yada zango ne a birnin Abuja na Najeriya, inda aka gudanar da gagarumin bikin karrama tsoffin 'yan wasan da suka kwashe tsawon rayuwar kuruciyarsu wajen hidimta wa kasar tare da daga martabarta a idon duniya. Gwamnati ta bada kyautukan ne ga tsoffin 'yan wasa 60 a daidai lokacin da ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.