Wasanni

Van Dijk na cikin mummunan hali

Virgil van Dijk ya samu mummunan rauni a wasan da Liverpool ta yi da Everton a ranar Asabar
Virgil van Dijk ya samu mummunan rauni a wasan da Liverpool ta yi da Everton a ranar Asabar Laurence Griffiths/Reuters

Dan wasan baya na Liverpool Virgil van Dijk ya bayyana fatan komawa fagen tamaula cike da karsashi bayan ya samu mummunan rauni a guiwra kafarsa a wasan da suka tashi 2-2 da Everton a ranar Asabar, yayin da jami’an kiwon lafiya suka ce, sai an yi masa tiyata.

Talla

Dan wasan mai shekaru 29 dan asalin Netherlands ya fice daga wasan na ranar Asabar sakamakon raunin wanda ya samu a daliln kalubalantar mai tsaren ragar Everton, Jordan Pickford.

Kawo yanzu babu cikakken bayani game da tsawon lokacin da van Dijk zai dauka na jinya, amma dai likitoci sun tabbatar cewa, raunin nasa ya munana.

Sai dai dan wasan ya bayyana a shafin sada zumunta cewa, a shirye yake ya tunkari duk wani kalubale.

Dan wasan ya kara da cewa, yanzu haka ya mayar da hankalinsa kan murmurewarsa kuma zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya koma fagen tamaula akan lokaci a cewarsa.

Van Dijk na cikin zaratan ‘yan wasan da Liverpool ke tunkaho da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.