Wasanni-Kwallon kafa

Da yiwuwar Liverpool ta karkare wasannin bana ba tare da van Dijk ba

Mai tsaron bayan Liverpool Virgil van Dijk
Mai tsaron bayan Liverpool Virgil van Dijk Reuters

Da alamu kungiyar kwallon kafa ta Liverpool za ta ci dogon zango cikin wannan kaka ba tare da mai tsaron bayanta lamba day aba wato Virgil van Dijk bayan raunin da ya samu a gwiwa yayin wasan tawagar na Asabar din da ta gabata.

Talla

Wasu bayanai na nuna cewa dan wasan wanda yanzu haka ke bukatar tiyata zai iya shafe tsawon wa’adin da ya rage cikin wannan kaka gabanin murmurewa, sai dai Liverpool a sanarwar da ta fitar ta ce akwai kwarin gwiwar van Dijk ya murmure gabanin karkare wasannin wannan kaka.

A kalaman Jurgen Klopp game da raunin na van Dijk kocin na Liverpool ya kwatanta rashin lafiyar mai tsaron bayan ga Club din tamkar matar da ke jiran mijinta ya fito daga kaso.

Yayin wasan Liverpool da Everton na ranar Asabar ne dai, van Dijk ya yi wata muguwar gumuwa da Jordan Pickford mai tsaron ragar Everton wanda kuma nan take ya samu gurdewar jijiyar gwiwa da ta kai ga cire shi daga filin wasa.

Baya ga gibin da zai haifarwa Liverpool, rashin lafiyar ta Van Dijk captin din Netherland za kuma ta hana shi takawa kasarsa Leda a wasannin Euro 2020 da ke tunkarowa.

Rashin mai tsaron bayan na Liverpool dai zai haddasawa Liverpool babban gibin da Jurgen Klopp zai fuskanci matsalar samun mai cike shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.