Wasanni-Kwallon kafa

Hankalina bai tashi ba duk da sukar da Ozil yayi - Arteta

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta tare da Pep Guardiola Manajan Manchester City.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta tare da Pep Guardiola Manajan Manchester City. Getty Images

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce babu abin da ya daga mai hankali, kuma lamirinsa a natse,  biyo bayan soke sunan Ozil daga cikin jerin ‘yan wasan da za su buga wa kungiyar wasannin gasar Firimiyar Ingila, inda ya ce abin da ya auku ba shi da nasaba da kin yarda da dan wasan ya yi a rage mai albashi.

Talla

Arteta yana mayar da martani ne ga Ozil bisa kalaman da ya yi a Larabar nan, inda yake bayyana takaicinsa kan abin da ya kira 'karancin aminci' bayan da aka shaida mai cewa ba za a yi masa rajista don fafatawa a gasar Firimiya ba.

Arteta ya ce matakin da ya dauka ba don kiyayya bane, illa saboda abin da ya shafi sana’ar kwallon kafa, yana mai cewa kowa na da ‘yancin fadin albarkacin bakinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.