Wasanni-Kwallon kafa

Messi ke hana Griezmann haskawa a Barcelona - Wenger

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsenal Wenger
Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsenal Wenger Reuters/Scott Heppell

Tsohon mai horar da ‘yan wasan Arsenal, Arsene Wenger ya ce Antoine Griezmann baya iya tabuka abin kirki a Barcelona saboda kasancewa Lionel Messi ya dishe haskensa.

Talla

Griezmann ya koma Barcelona daga Atletico Madrid a karshen kakar wasan shekarar 2019 bayan da ya shahara a Atletico din.

Bayan ya ci kwallaye 20 a kowace kaka a cikin kakannin wasa 6 da ya zauna Atletico, Griezmann ya zura kwallaye 15 ne kawai a wasanni 48 a kakarsa ta farko a Barca.

Har yanzu dan wasan gaban bai saka kwallo a raga ba a wasanni 4 da ya buga wa Barca a wannan kaka a gasar La Liga, amma Wenger na ganin cewa yana da sauran gudummawar da zai bayar a kungiyar, saboda bata kare mai ba.

Wenger ya ce wani dalilin rashin yin katabus din sa ma shine sanya shi a gurbin da bai saba bugawa ba a filin kwallo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI