Wasanni-Kwallon kafa

Zidane ya dau alhakin lallasa Madrid Shakhtar ta yi

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane.
Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane. REUTERS/Charles Platiau

Mai horar da ‘yan wasan Real Madrid, Zinedine Zidane ya karbi laifi a a game da rashin nasarar da suka yi har gida a hannun Shakhtar Donetsk a wasan gasar zakarun nahiyar Turai.

Talla

Zakarun na gasar Ukraine sun isa Madrid ne ba tare da manyan ‘yan wasansu masu bugawa a tawagar farko guda 13 ba, bayan da cutar coronavirus ta harbi ‘yan wasansu 19, lamarin da ya bar su da matasa daga karamar tawagarsu.

Sai dai duk haka matasan na Koch Luis Castro ba su yi kasa a gwiwa ba , inda suka antaya wa Real Madrid kwallaye 3 a raga tun a farkon wasan da aka fafata a filin atisayen Madrid na Alfredo di Stefano.

‘yan wasan Madrid dai sun yunkuro, inda Luka Modric da Vinicius suka saka kwallo daya a raga kowanne, amma hakan bai samar wa kungiyar da ta lashe gasar zakarun Turai har sau 13 mafita ba, wasa ya tashi 2-3.

Wannan rashin nasarar na zuwa ne bayan Madrid din ta sha ci daya mai ban haushi a hannun sabbin shiga La Liga, Cadiz a ranar Asabar.

Zidane ya ce bai ida dora tawagar a kan seti kamar yadda yake so ba, saboda haka ya dau alhakin wannan rashin nasara.

Zidane, wanda shahararren tsohon dan wasan Madrid ne, ya lashe wannan kofi na Zakarun Turai sau 3 a jere a cikin shekaru 3 na farko da ya yi yana horar da tawagar Real Madrid, amma shawarar da ya yanke ta hutar da wasu ‘yan wasa saboda karawar hamayyar Elclasico tsakaninsu da Barcelona a Asabar mai zuwa ta dama mai lissafi.

Kyaftin Sergio Ramos bai buga wannan wasa ba sakamakon rauni da ya ji a guiwar kafarsa, abin da ya sa kenan ma Madrid ta samu babbar matsala a bayanta, inda ‘yan wasan bayan suka kasa hana Mateus Tete da Manor Solomon cin kwallaye biyu, bayan Raphael Varane ya ci gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.