Wasanni

Barcelona ta zargi VAR da yi mata keta a wasanninta

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona bayan shan kaye a gasar La Liga.
Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona bayan shan kaye a gasar La Liga. Reuters

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Ronald Koeman ya ce lokaci ya yi da duniyar kwallo za ta fahimci ketar da na’urar taimakawa alkalin wasa ta VAR ke yiwa tawagarsa.

Talla

Koeman wanda ke wannan korafi bayan shan kayensu har gida a hannun Real Madrid da kwallaye 3 da 1 karkashin gasar La Liga a karshen makon nan, ya ce cikin wasanni 5 da suka gudana a ranar da suka sha kayen a wasansu ne kadai VAR ta yi aiki.

A cewar Koeman kowacce tawaga na iya yin abin da taga dama kuma VAR ta kawar da kai sabanin Barcelona, domin kuwa idon na’urar da kansu.

Koeman wanda ya alakanta rashin nasarar ta Barcelona a hannun Real Madrid da ketar VAR ya ce yana da kwarin gwiwar tawagar tasa za ta bayar da mamaki.

Ko a bara ma dai Real Madrid ce ta lashe wasannin da ya gudana tsakanin kungiyoyin biyu tare da dage kofin na La Liga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.