Wasanni-Kwallon kafa

Pogba ya musanta ritaya daga takawa Faransa leda

Dan wasan tsakiyar tawagar kwallon kafar Faransa Paul Pogba bayan lashe kofin Duniya a Rasha.
Dan wasan tsakiyar tawagar kwallon kafar Faransa Paul Pogba bayan lashe kofin Duniya a Rasha. AFP/ FRANCK FIFE

Dan wasan Faransa da ke taka leda a Manchester United Paul Pogba ya musanta labaran da ke cewa ya yi ritaya daga tawagar kwallon kafar kasar biyo bayan kalaman batancin da shugaban kasar Emmanuel Macron ya yiwa addinin Islama.

Talla

Sakon da ya wallafa a Twitter, Pogba wanda ya sauya addininsa zuwa musulunci ya bayyana labarin da kanzon kurege.

Wasu bayanai da jaridar The Sun ta wallafa ta ce Pogba wanda ya lashe kofin Duniya ya fusata da kalaman na Macron inda ya dauki matakin don zamowa martanin ga kasar ta Faransa, sai dai cikin gaggawa dan wasan ya musanta batun.

Tun farko dai Faransar ta fitar da zanen batanci ga Annabin Rahma wanda kuma shugaban kasar ya kare mawallafan zanen yayinda kuma ya sha alwashin kawo karshen zafin addinin Islama a kasar biyo bayan yadda wani Dalibi musulmi ya fille kan malaminsa bayanda ya nuna zanen batancin a ajinsu.

Pogba ya bayyana cewa a shirye ya ke ya taka leda karkashin tawagar ta Faransa a karawarsu da Findland ranar 11 ga watan Nuwamba mai kamawa gabanin haduwarsu da Portugal da Sweden karkashin Nations League.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.