Wasanni-Dambe

Zakaran LFC Khabib Nurmagomedov ya yi ritaya bayan nasara kan Justin Gaethje

Mai rike da kambun LFC Khabib Nurmagomedov.
Mai rike da kambun LFC Khabib Nurmagomedov. REUTERS/Said Tsarnayev

Zakaran damben boxing na LFC da ke karkashin MMA ta Amurka Khabib Nurmagomedov dan kasar Rasha ya sanar da ritaya daga fagen damben bayan nasararsa kan Justin Gaethje a wasansa na 29 ba tare da an taba nasara kansa ba. 

Talla

Bayan nasara kan Gaethje dan Amurka a fadan wanda aka sanyawa tsabar kudi da ya gudana a tsibirin Yas na hadaddiyar daular larabawa cikin daren Asabar din da ta gabata, Khabib dan yankin Dagestan a kasar Rasha mai shekaru 32 wanda ba a taba nasara kansa ba cikin fada 29 da ya yi a matakin Duniya, ya ce yana fatan kammala wasannin na MMA ba tare da anyi nasara kansa ba.

Nurmagomedov wanda ya rasa mahaifinsa kuma Kocinsa Abdulmanap Nurmagomedov watanni kalilan da suka gabata sanadiyyar Covid-19, jim kadan bayan bayyana shi a wanda ya yi nasara a karawar wadda ta kai ga Gaethje ya mika, nan ta ke Khabib ya sadaukar da wasan ga mahaifinsa tare kuma da bayyana ritayarsa.

A cewar Khabib ya yi nasarar cikawa mahifansa biyu burinsu, domin kuwa Mahifinsa na fatan ya kai babban mataki a damben a fagen Duniya yayinda mahaifiyarsa kuma sam bata son damben, inda ya je ya yi ritayarne don faranta ran mahaifiyarsa.

A tsawon lokacin da ya dauka yana dambe, Khabib mai shekaru 32 ya dambace da gwarazan 'yan Dambe na Duniya ciki har da Dustin Poirer da Cornor McGregor da Edson Barboza da Micheal Johnson baya ga Rafael Dos Anjos.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.