Wasanni-Kwallon kafa

Alkalan wasa ba su da uzurin yin kuskure tun da akwai VAR - Mourinho

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham José Mourinho.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham José Mourinho. REUTERS/John Sibley/File

Kocin Tottenham, Jose Mourinho ya caccaki irin kurakuran da ake yi wajen yanke hukunci a wasanni duk da akwai na’urar VAR, mai taimaka wa alkalin wasa, yana mai cewa babu wani uzuri da alkalan wasa za su bayar na yin kuskure saboda yanzu akwai fasahar da ke taimaka musu.

Talla

Na’urar VAR ta sake jan magana bayan da ta yanke hukunce hukunce da suka janyo cece kuce a karshen makon da ya gabata yayin wasan hamayya na Everton da Liverpool, da wasan gasar zakarun nahiyar Turai tsakanin Manchester City da Porto a ranar Laraba.

Na’urar VAR ba ta kama mai tsaron ragar Everton Jordan Pickford da laifi ba bayan da baro baro ya rafke dan wasan baya na Liverpool Virgil van Dijk har sai da ya tafi doguwar jinya sakamakon mummunan rauni a gwiwar kafarsa.

A wasan tsakiyar makon da ya gabata, dan wasan City Ilkay Gundogan ya cancanci jan kati amma ba a ba shi ba duk da make mai tsaron ragar Porto Agustin Marchesin, amma kuma aka baiwa City bugun daga kai sai mai tsaron raga sakamakon rafka da Pepe ya yi bayan lamarin.

Sai da na’urar VAR ta waiwaya ta dubi abubuwan da suka faru amma kuma ta dau irin hukuncin da ta dauka.

Mourinho ya ce kamata ya yi a bai wa mai tsaron ragar Everton Pickford da Gundogan na City jan kati tun da akwai VAR, duba da cewa alkalin wasa bai ga abin da ya faru ba a yayin da ya faru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.