Babu wanda zai iya tabuka rabin abin da Messi da Ronaldo suka yi a kwallon kafa - Maradona
Wallafawa ranar:
Diego Maradona ya ce Lionel Messi da Cristiano Ronaldo sun yi wa sauran ‘yan wasa zarra, kuma baya tsammanin akwai wani dan wasan da zai yi rabin abin da suka tsinana a wasan tamola.
Diego Maradona ya ce Lionel Messi da Cristiano Ronaldo sun yi wa sauran ‘yan wasa zarra, kuma baya tsammanin akwai wani dan wasan da zai yi rabin abin da suka tsinana a wasan tamola.
Shi kansa Maradona ana mai kallon daya daga cikin manyan ‘yan wasan da aka taba samu a fagen kwallon kafa, bayan ya taka rawar gani a harkar, inda ya lashe kofuna a Barcelona da Napoli, sannan ya lashe kofin duniya a shekarar 1986 da kasarsa Argentina a Mexico.
‘Yan wasa kalilan ne suka zo kusa da Maradona a wannan harka, sai dai Messi da Ronaldo sun bi sahun ‘yan wasan da za a ce duniyar kwallon kafa na alfahari da su.
Ba a yi mamaki ba da Maradona ya zabi Messi da Ronaldo a lokaci da aka ce ya zabi yan wasa biyu da suka yi wa sa’o’insu zarra a wasan kwallon kafa na zamani.
Da yake tsokaci, ta wajen tuna baya a kan irin rawar da ya taka a wasan kwallon kafa, gabanin cikarsa shekaru 60 a karshen wannan wata da muke ciki, Maradona, cikin raha, ya ce zai so a ce ya sake jefa kwallo da hannu a ragar Ingila, sai dai wannan karo da hannun dama.
Maradona ya tuno ne da kwallon da ya saka a ragar Ingila da hannu, a yayin wasan cin kofin duniya a Mexico a shekarar 1986
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu