Wasanni-Kwallon kafa

Kwallaye biyun da Ibrahimovic ya ci ba su hana AC Milan canjaras da Roma ba

Dan wasan AC Milan Zlatan Ibrahimovic.
Dan wasan AC Milan Zlatan Ibrahimovic. REUTERS/Alessandro Garofalo

Zlatan Ibrahimovic ci kwallaye biyu amma basu hana AC Milan yin canjaras a karon farko a wannan kaka a wasan da suka tashi 3-3 da Roma ba.

Talla

Ibrahimovic, mai shekau 39, ya ci wa AC Milan kwallon farko a wasan kafin abokin hamayarsa Edin Dzeko ya farke wa Roma.

Alexis Saelemaekers ya sake sanya Milan a gaba da kwallon daya kara, amma kuma Jordan Veretout ya farke ta daga bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Ibrahimovic ya maida wasan 3-2 daga bugun daga kai sai mai tsaron raga da suka samu amma kusan karshen wasa Marash Kumbulla na Roma ya cire wa Roma kitse a wuta, aka tashi ba kare bin damo, lamarin da ya hana Milan rawar gaban hantsi.

Har yanzu dai Milan ce a kan gaba a teburin Seria A, Napoli na biye.

Kwallaye 5 Ibrahimovic, wanda a farkon wannan wata ya harbu da cutar Coronavirus ya ci daga wasanni 6 a wannan kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.