Wasanni-Kwallon kafa

Sai an kusa karkare wasa Zidane yake saka ni - Isco

Isco na Real Madrid.
Isco na Real Madrid. REUTERS/Juan Medina

Isco ya caccaki mai horar da ‘yan wasan Real Madrid, Zinedine Zidane, yana mai cewa dan kasar Faransan ya maida shi saniyar ware.

Talla

Dan wasan tsakiyar na kasar Spain bai fafata a wasan hamayya na El Clasico da Madrid ta lallasa Barcelona da ci 2-3 ba ranar Asabar, da ma rashin nasarar da suka yi a hannu Shakhtar Donetsk 3-2 a wasan gasar zakarun nahiyar Turai kwanaki uku kafin El Clasico.

Ba shakka dan wasan bai samu fafatawa a wasanni dayawa wa kungiyarsa ba, saboda wasanni 4 kawai ya buga tun bayan dawowa daga jinyar raunin da ya ji a idon sawu, kuma yanayi ne da yake matukar bata wa dan wasan rai.

A cikin shekaru 7 da ya yi a kungiyar Real Madrid, Isco bai samu cikakkiyar damar duk da kokarin da yake yi, har ma wasu na cewa bai cika taimaka wa ‘yan wasan baya kamar yadda ya dace bane, shi ya sa Zidane bai cika saka shi a wasa ba.

Yanzu haka Real Madrid na matsayi na 2 a teburin La Ligar Spain da maki 3, suna biye da Real Sociedad, wacce ke ta daya kenan a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.